19 Satumba 2020 - 11:10
​An Shelanta yau A Matsayin Ranar Fushi A Falastinu A Kan Masu Kulla Hulda Da Isra’ila

Jagororin kungiyoyin Falastinawa sun shelanta ranar yau Juma’a a matsayin ranar fushi ga dukkanin al’ummar Falastinu, domin nuna takaici kan yadda wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suka mika kai ga yahudawan Isra’ila.

ABNA24 : Rahotanni daga Falastinu na cewa, bayan sanarwar da jagororin kungiyoyin falastinawa suka bayar, a yau Juma’a al’ummar Falastinu suna gudanar da zanga-zanga da jerin gwano domin yin tir da Allawadai da gwamnatocin kasashen larabawa da suka kulla hulda da Isra’ila a hukumance kuma a bayyane.

Bayanin jagororin Falastinawan ya bayyana ranar yau Juma’a a matsayin ranar makoki, a kan aka bukaci Falstinawa da su daga bakaken tutoci a dukkanin yankunan Falastinawa, domin nuna bakin ciki a kan ha’inci na shugabannin larabawan da suka dauki wannan mataki.

Al’ummar Falastinu na kallon wannan matakia a mtsayin wani shiri na kawar da hankulan al’ummomin duniya daga irin halin da suke ciki, da kuma mamayar kasarsu da Isra’ila ke yi, da sauran matakai na cin zarafi da kisa da suke fuskanta kullum rana, gami da keta alfarmar wurare masu tsarki na addinin muslucni da Isra’ila ke yi, inda wadannan gwamnatocin larabawan ba su taimaka musu ba, maimakon haka ma sai dai hada baki da yahudawan domin aiwatar da manufarsu a kan Falastinawa.

/